<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>284</hymn_number>
<title>Ya Almasihu, Sarkin Tsarkakanka LW284</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Almasihu, sarkin tsarkakanka,
 Kai ne ka taya su cikin jaraba.
 Duk Masu Binka suna yabonka.
 Halleluya! Halleluya!

[V2]
 2) Kai ne mazauninmu har abada,
 Kai fā na ceto ne da mai taimako.
 Kai Shugaba ne cikin yaƙinmu.
 Halleluya! Halleluya!

[V3]
 3) Idan da tsoro cikin zukatanmu,
 Ko ikon Shaiɗan ne ya ke ƃata rai,
 Kai ne ka fi shi, kai kuwa namu ne.
 Halleluya! Halleluya!

[V4]
 4) Kai ne ka kira mu mu bi bayanka.
 Kai za ka taya mu cikin yaƙin nan.
 Shaiɗan, magauci, za ka taka shi.
 Halleluya! Halleluya !

[V5]
 5) Sai wata rana sammai za su buɗe,
 Za ka bayyana nan cikin daraja.
 Mu kuwa magada ne na muikinka.
 Halleluya! Halleluya!</lyrics>
</song>